Posts

Showing posts from September 8, 2025

Hadiths six to ten from imam Ali (as)

Assalamu alaikum ga cigaban hadiths five :  6-Imam Ali [AS] ya ce, “Mafificin ayyuka sune wa]anda ka tilasta kanka wajen aikatasu.” Wato ayyukan da mutum yayi mujahada wajen aikatasu,ayyukan na ibada ne ko umarni ko hani. 7-Imam Ali[AS] ya ce, “Ina mamakin wanda yake cire tsamanni daga rahamar Allah Ta’ala alhali ga istigfari.” 8-Imam Ali [AS] ya ce, “Allah Ta’ala yana da hakki ga kowace ni’ima da yayi ma mutum,wanda ya bada hakkin sai Allah ya kara masa,wanda kuma bai bayar ba to akwai yiyuwar ni’imar ta gushe.”Hakkin ko wace ni’ima da Allah yayi ma mutum shine godiya ga Allah kanta,ya kuma kasance ka da mutum yayi amfani da ni’imar da Allah yayi masa wajen saba masa. 9-Imam Ali [AS] ya ce, “Duk wanda aikinsa ya maida shi baya to nasabarsa ba zata kaishi gaba ba.”Wato idan mutum bai yi kyakkyawan aiki ba a wannan gida na duniya to ranar lahira nasabarsa ba zata amfane shi ba.” 10-Imam Ali [AS] ya ce, “Kuji tsoron saba ma Allah a boye domin mai ganin boyen shine zai yi hukunci rana...